Tawagar Hukumar kwastam ta kasa ta kai ziyarar jaje ga al’umomin da fashewar tunkunyar iskar gas ya shafa a garin Babura na jihar Jigawa.

A fadar Hakimin Babura, kwantirolan hukumar mai kula da jihohin Kano da Jigawa MA Raji ya bayyana hadarin a matsayin abin takaici.

Ya kuma yi adduar Allah ya kiyaye afkuwar lamarin anan gaba

MA Raji ya ce zasu cigaba da horas ma’aikatansu domin kara samun kwarewar aiki

A jawabansu daban-daban, shugaban karamar Hukumar Babura Alhaji Lawal Isma’ila da kuma Hakimin Babura Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, sun bukaci kwantirolan da ya tilastawa ma’aikatan kwastam daina harbin mutanen da suke zargin yan fasa kwauri ne.

Sun kuma bukaci hukumar kwastam da ta tallafawa wadanda iftilain fashewar gas din ya shafa tare hukunta ma’aikatan da suka haddasa faruwar lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: