Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta samar da ruwan sha da sauran ayyukan more rayuwa a fadin Jihar

0 87

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta samar da ruwan sha da sauran ayyukan more rayuwa a fadin Jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa na Jihar, Malam Garba Yusuf, shine ya bayyana hakan a wata hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a Kano.

Ya ce saboda yawan ƴan gudun hijirar da su ke shigowa daga garuruwan da ƴan fashin daji su ka addabesu a jihohin da ke maƙwabtaka da Kano, da kuma yawan ababen more rayuwa da ake da su a fadin jihar ya taimaka wajen ƙaruwar masu buƙatar ruwan.

A cewarsa, lokacin da aka gina matatar ruwa ta Challawa, bukatar ruwa a Kano ta kai Lita Miliyan huɗu a kowacce rana, inda ya ƙara da cewa yanzu haka bukatar ta karu zuwa lita miliyan 200 a kowace rana.

Yusuf ya ƙara da cewa ma’aikatar ta na da sashen ban ruwa ga madatsun ruwa da ke kula da ayyukan ban ruwa da kuma bayar da gudummawar gaske wajen samar da abinci a fadin jihar.

Ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitin da zai wayar da kan jama’a don sanin cewa ana biyan kudin ruwa kamar yadda ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: