Hukumar Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golden Stars ta kori Babban Kocin kungiyar da mataimakan sa biyu

0 250

Hukumar Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golden Stars, ta kori Babban Kocin kungiyar, Gilbert Okpana da mataimakansa biyu, Auwalu Bade da Abdulaziz Adeza.

Sakataren kulob din, Jafaru Mohammed, a cikin wata sanarwa a jiya, ya ce sallamar masu horarwar ta fara aiki nan take.

Jafaru Mohammed ya ce an umarci Ado Suleiman da Yakubu Umar Aleka, da su zama babban koci da mataimaki.

A cewarsa, Babangida Mohammed zai cigaba da zama mai horas da masu tsaron ragar kungiyar.

Sakataren ya kara da cewa kwamitin gudanarwar kungiyar ya amince da hutun makonni hudu ga dukkan ‘yan wasa da masu horas da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: