Hukumar Kwastam ta kama buhunan shinkafa ta ƙasar waje fiye da dubu ɗaya da sauran kayan da suka kai fiye da biliyan 20 a jihar Jigawa

0 375

Hukumar Kwastam ta kasa, reshen jihar Kano da Jigawa, ta bayyana cewa ta tara kudaden shiga da ya kai Naira bilyan 25 da milyan 3 a shekarar 2021, kari akan wanda hukumar ta tara a shekarar data gabata na N24.4billion.

Hukumar tace ayyukan da take yi a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano ya kara habaka kudaden shigar ta.

Kwanturolan hukumar, Suleiman Pai Umar ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, rundunar ta kuma samu nasarar dakile ayyukan fasa-kwaurin da ta kai ga kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai sama da Naira milyan 187m a ayyukan ta na baya-bayan nan.

Ya ce, kayayyakin da hukumar ta kama sun hada da buhunan shinkafa 1040 na kasar waje na kimanin naira miliyan 69, da spaghetti ta kasashen waje da darajarsu ta kai Naira miliyan 63.9 da sauran kayayyaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: