Hukumar asusun kiwon lafiya ta jihar Jigawa ta kammala yiwa masu karamin karfi da masu rauni da zasu amfana da shirin bada magani kyauta rijistar mallakar katin shedar zama dan kasa a karamar Hukumar Dutse.


Sakataren zartarwa na asusun Dr Nura Ibrahim ya sanar da hakan ta cikin shrin radio Jigawa na mako mako mai suna Fitila.

Yace hukumar bada katin shedar zama dan kasa ta jiha ta basu aron maaikata bakwai domin yiwa masu karamin karfi da masu rauni da zasu amfana da shirin bada magani kyauta rijistar katin shedar zama dan kasa.


Da ya juya ga shirin yiwa maaikatan jiha da kananan hukumomi dana sashen ilmi rijistar shiga shirin bada magani kyauta , Dr Nura Ibrahim ya kara da cewar aikin rijistar maaikatan na samun nasarar da ake bukata a cibiyoyin lafiyar da maaikata suka bukaci yin hakan.


Yace tuni wasu maaikatan suka fara amfana da shirin kula da maganin kyauta inda ya bukaci duk wani maaikaci mai korafi daya gabatar dashi ga hukumar
Yayinda hukumar take cigaba da rijistar maaikata masu san shiga shirin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: