‘Yan Niger Delta sunsha alwashin kai hari a Abuja da Lagos

0 114

Yan Najeriya sun soma yin raddi bayan da wasu ‘yan kungiyar da ke fafutuka a yankin Naija Delta suka sha alwashin kai hari a biranen Lagos da Abuja.

A wani bidiyo da kungiyar da ake kira Supreme Egbesu Liberation Fighters ta wallafa a shafin Youtube ranar Talata ta yi zargin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari tana dakile ci gaban yankin sannan ta gaza wajen shirinta na yin afuwa ga mayakan Naija Delta.

An nuno ‘ya’yan kungiyar fuskarsu a rufe da kyalle inda daya daga cikinsu yake karanta sanarwar da ta zargi gwamnatin tarayya da siyasantar da lamarin share dagwalon mai na yankin Ogoni, yana mai cewa ba ta gina makarantu da samar da ruwan sha da asibitoci da sauran ababen roye rayuwa ba.

A cewarsa, maimakon samar da ababen more rayuwa, gwamnati ta jibge sojoji da jiragen ruwan yaki da makamantansu domin cin zarafin mazauna yankin.

“Amma babu damuwa, saboda za mu zo mu lalata dukkan abubuwan da aka gina a Abuja da Lagos. A matsayinmu na kungiyar da ke fafutukar ‘yanto mutanenmu, za mu lalata rijiyoyin mai na kan tudu da na karkashin kasa nan ba da jimawa ba, za mu durkusar da tattalin arzikin Najeriya,” in ji shi.

Shafin Twitter ‘ya kama da wuta’

Sai dai wannan barazana da wasu daga cikin masu fafutukar yankin Naija Delta suka yi ta ja hankalin ‘yan Najeriya musamman wadanda ke amfani da shafin Twitter.

Hakan ya sa suka rika amfani da maudu’in “Lagos and Abuja” domin bayyana ra’ayoyinsu kan batun.

Wata mace da ke amfani Twitter, Olayemi, ta ce ya kamata masu fafutukar yankin na Naija Delta su yi amfani da makamansu wajen yakar ‘yan fashin daji da miyagun makiyaya maimakon kai hari kan Lagos da Abuja.

A cewarta: “Me ya sa suke barazanar kai hari a Lagos da Abuja? Maimakon su (mayakan) su rika tsara yadda za su kai hari kan ‘yan fashin daji da miyagun makiyaya, sun zabi kai hari kan mutanen da ba su da laifi.”

Why threaten to attack Lagos and Abuja? Instead of them (militants) to be planning to attack bandits and criminal herders, it is peaceful people they chose to attack. Nonsense! pic.twitter.com/3wsH078i9w— Olayemi 🇳🇬 (@olayemi_123) February 24, 2021

Shi kuma wani mai suna Kwam ya ce mayakan Naija Delta sun yi barazanar kai hari a Lagos da Abuja ne saboda yadda gwamnatin Najeriya take tafiyar da lamuran ‘yan fashin daji da masu satar mutane a yanin arewa maso yammacin kasar.

Niger delta militants threatening to destroy Lagos and Abuja is basically because they see the way this current administration is handling issues with bandits and terrorist. https://t.co/mKp7Dn9sSb— K W A M (@thiskwam) February 24, 2021

A nasa bangaren, Baller G, ya mayar da batun abin wasa inda ya yi tambayar cewa: “Idan masu fafutukar ynakin Naija Delta suka kai hari a Lagos da Abuja, wacce jiha kuke gani Buhari zai mayar babban birnin tarayyar kasar nan?”

If these militants takes over Lagos and Abuja, which state do u think Buhari will make the capital of Nigeria?— Baller G (@spunky_niga) February 24, 2021

Sharhi

Ayyukan masu hakar man fetur sun lalata albarkatun kasar yankin
Bayanan hoto, Ayyukan masu hakar man fetur sun lalata albarkatun kasar yankin

Rikicin masu tayar da kayar baya a yankin Naija Delta ya lafa sosai tun bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya Umaru Musa Yar’adua ya yi musu afuwa sannan.

Kazalika gwamnatocin da suka biyo baya musamman gwamnatin Shugaba Buhari ta dauki alhakin share dagwalon da ayyukan kamfanonin da ke hakar man fetur sua jawo.

Sai dai duk da haka wasu na ganin dole gwamnati ta kara sanya ido da tabbatar da cewa mazauna yankin da ake hakar man sun ci moriyar albarkatun kasar da suke hakowa.

Masu sharhi kan lamuran tsaro na ganin barazanar masu fafutukar yankin Naija Deltan za ta kara zaman dar-dar din da ake yi kan halin da ake ciki a kasar, sakamakon hare-haren ‘yan fashin daji da na mayakan Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

BBCHAUSA ne suka wallafa asalin labarin;

https://www.bbc.com/hausa/labarai-56165957

Leave a Reply

%d bloggers like this: