Hukumar NDLEA reshen jihar Jigawa ta kama mutane 48 da ke safarar miyagun kwayoyi a fadin jihar

0 77

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen jihar Jigawa, ta ce ta kama wasu mutane 48 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jiharnan.

Kwamandan NDLEA a jihar Jigawa Hajiya Maryam Gambo, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau a Dutse.

Maryam Gambo ta ce an kama wadanda ake zargin ne a wani samame na musamman da aka gudanar a kananan hukumomi biyar na jihar, wadanda ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Ta bayyana cewa an gudanar da ayyukan ne tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, a kokarin da ake na dakile matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Kwamandan ta kara da cewa za a fadada aikin zuwa sauran kananan hukumomi 22 na jihar, a wani mataki na kakkabe wuraren da ake zargin mashaya ne a jihar baki daya.

A cewarta, masu amfani da muggan kwayoyi ko masu aikata laifuka daga cikin mutane 48 da aka kama, an sanya su a ajin bayar da shawarwari na mako-mako ko wata-wata, bisa la’akari da matakin shaye-shayensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: