Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yankewa wani dan kungiyyar Boko Haram hukuncin kisa ta hanyar rataya

0 142

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yankewa wani dan kungiyyar Boko Haram Abdulsalam Adinoyi hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kafin hakan dai an gurfanar Adinoyi ne bisa zargin aikata laifuka biyar, wandada suka hada da fashi da makami, kisan kai, ta’addanci da kuma mallakar makamai ta barauniyar hanya.

cikin kunshin tuhume tuhumen da akayiwa Adinoyi, wanda dan asalin garin Okene ne dake jihar Kogi, an kamashi da laifun kashe wani jmai’in dan Dan sanda da ake kira Gana Jiya, wanda suka bude masa wuta a shingen jami’an yansanda dake oye na jihar Ekiti.

Haka kuma Adinoyi bayan ya kashe jami’in dan sandan, ya raunata sauran jami’an yansanda da Harbin bindiga.

Hakan ya faru ne tin daga ranar 22 ga watan Disamba na 2016 zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2017.

A lokacin dayake amsa laifunsa, Adinoyi, yace lokacin da jami’an yansan suka kamashi a gidansa ansamu bindiga AK-47 a hannunsa kuma shi da abokanansa Abu Uwais da Aminu wanda akafi sani da suna Idi-Amin, suna shirin kaddamar da wani hari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: