Hukumar NDLEA ta kuɓutar da ƙananan yara 34 da akai safarar su daga Arewa a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja ta jihar Kogi

0 188

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa NDLEA ta kubutar da kananan yara 34 a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi.

Kakakin hukumar Femi Babafemi shine ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumar ta kwace sassan karafunan bindiga a jihar Anambra.

A cewar sanarwar yaran da hakumarta kubutar sun kasance tsakanin shekaru 8 zuwa shekara 14, wadanda akayi safararsu ba bisa ka’ida ba daga jihar Ogun zuwa birnin tarayya Abuja.

Yace da fari anyi safarar yaran daga jihar pilato zuwa jihar Ondon, inda daga nan ne aka kacancanasu ga magenta a matsayin yan aikatau.

Da yake jawabi shugaban hukumar Brigadier-General Buba Marwa mai ritayam, ya jinjinawa tawagar jamian hukumar bisa aiki tukuri da kuma hadin kai tsakaninsu da sauran jamian tsaro wajen yaki da matsalar tsaro a fannin su.

Kazalika Brigadier-Genar Marwa ya bada umarnin mayar da yara 34n da aka yi safara dasu zuwa hukumar yaki da safarar mutane ta kasa NAPTIP domin daukar mataki na gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: