Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce ta karɓi ‘yan Najeriya 203 da aka kwaso daga Libya bayan sun kasa fitowa daga ƙasar ta arewacin Afirka.
Jim kaɗan bayan isarsu filin jirgin sama na Murtala Muhammed a Legas a ranar Litinin, jami’an hukumar ta tarɓe su.
Jirgin kamfanin Al Buraq ne ya kwaso mutanen, waɗanda suka ƙunshi maza manya 50, mata manya 96, da yara 29, da kuma jarirai 28.
Ƙungiyar kula da ƙaura ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin mayar da su gida bisa haɗin gwiwa da hukumar NEMA da sauran hukumomi.
Wata sanarwa da NEMA ta fitar a jiya Talata ta ce biyu daga cikin mutanen na buƙatar kulawar gaggawa, kuma nan take aka kai su asibitin Ikeja domin duba su.