Kwamiti na jam’iyyar PDP ta yanke shawarar daukar matakin shari’a kan Sheriff Oborevwori

0 440

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jam’iyyar adawa ta PDP ya yanke shawarar daukar matakin shari’a kan Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wasu manyan jiga-jigai da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Wannan mataki ya biyo bayan wata doguwar ganawar sirri da ta dauki tsawon sa’o’i shida a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a jiya talata, inda shugabannin PDP suka umarci Lauyan Jam’iyyar na Ƙasa da ya fara shirye-shiryen kwato abin da suka kira satar iko a Jihar Delta.

A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron, jam’iyyar ta umurci Lauyan da ya dauki matakan shari’a domin kwato mulkin da jam’iyyar ke ikirarin mallaka daga hannun gwamnan da sauran wadanda suka sauya sheka daga PDP a jihar.

A kokarinta na farfado da karfinta a jihar, jam’iyyar ta naɗa Emma Ogidi, Shugaban Yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar, domin jagorantar al’amuran PDP a Jihar Delta tare da jagorancin shirin sake tsarawa da gina jam’iyyar a can.

Leave a Reply