Hukumar NEMA ta karbi yan Najeriya 111 da aka dawo da su daga jamhuriyar Nijar

0 250

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta karbi yan kasar 111 da aka dawo da su daga janhuriyar Nijar.

Kamar yadda hukumar ta wallafa a shafin ta na X, matakin ya kasance cikin shirin hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tare da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.

Tuni aka dauki cikakkun bayanan yan Nijeriyar wadanda suka kunshi maza 87 da mata 8, sai kuma kananan yara mata 9 da kuma kananan yara maza 8.

Leave a Reply