Najeriya Ta Kwato Dalolin da aka Sace an Dawo da $763.7m da £6.4m ga Gwamnati

0 523

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya bayyana cewa an dawo da wasu daga cikin kuɗin Najeriya da aka sace, Ya bayyana cewa kuɗin da aka samu nasarar dawo da su asusun gwamnati sun kai $763,734,000 da £6,472,610 da aka sace daga Najeriya tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024.

Daily Trust ta ruwaito cewa Fagbemi ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe taro kan dawo da dukiyoyi da ma’aikatarsa ta shirya mai taken: “Haɗin gwiwa domin dawo da dukiyoyi da sarrafa su yadda ya kamata.

Leave a Reply