Hukumar North West Development Commission ta fada cikin rikicin cikin gida sakamakon cece-kuce da ya biyo bayan wani shirin bayar da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje ga matasan Arewa maso Yamma.
Wasu mambobin kwamitin hukumar sun musanta cewa an taɓa tattauna batun a wani zama, inda suka ce wasu daga waje ne suka bullo da shirin ba tare da bin ƙa’ida ba.
Amma Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya ce an sanar da shugaban kwamitin tun ranar 28 ga Afrilu, yana mai cewa manufar ita ce taimaka wa matasa domin su dawo su bunƙasa yankinsu.
Shi kuwa shugaban kwamitin, Lawal Sama’ila Abdullahi, ya kira zaman gaggawa domin duba lamarin, yayin da Farfesa Ma’aji ke cewa wasu na ƙin jinin shirin ne saboda zai fi amfani ga ’ya’yan talakawa kuma ba a aika kowa ƙasashen waje ba tukuna, illa dai fara neman wadanda suka cancanta.