Hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan 7,000 wajen gudanar da ayyuka

0 87

Hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa, STOWA, tace ta kashe kudi fiye da naira miliyan dubu 7 wajen gudanar da ayyukanta daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Mukaddashin manajan daraktan hukumar, Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.

Yace a duk shekara hukumar tana kashe kudi fiye da naira miliyan dubu daya wajen gudanar da ayyukan samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwan jiharnan.

Adamu Garba ya kara da cewa ya zuwa yanzu hukumar ta sauya gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa masu amfani da hasken rana guda 209.

A cewarsa, hukumar ta gyara gidajen ruwa 750 daga cikin fiye da 1000 da take dasu a fadin jihar nan.

Adamu Garba ya danganta nasarorin da hukumar ta samu akan jagorancin gwamna Muhammad Badaru Abubakar da kuma kwamishinan albarkatun ruwa na jiha, Alhaji Ibrahim Garba Hannun-Giwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: