Hukumar Shige Da Fice Ta Kasa (NIS) Ta Bayyana Cewa Ta Cabke Wata Mata Kan Zargin Safarar Mutane

0 280

Hukumar Shige da Fice ta kasa (NIS) ta ce ta cafke wata da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mata shida a kan iyakar Seme–Badagry a jihar Lagos.

Kamun ya gudana ne karkashin hukumar shige da fice ta kasa reshen Seme a jihar Lagos, tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro, inda nan take aka kai su Shelkwatar hukumar ta NIS dake Zone A a Ikeja

Rahotanni sun ce an kama wata mata ‘yar shekara 24 mai suna Victor Jennifer daga jihar Benue, yayin da ake zarginta da yunkurin fitar da matan Najeriya shida masu shekaru tsakanin 20 zuwa 23 ba tare da sahalewar takardun tafiya ba.

Hukumar ta bayyana cewa an kai wadanda aka kama da wadanda aka ceto ofishin shiyya na hukumar NIS da ke Ikeja domin fara bincike, kafin daga bisani a mika su hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A cewar jami’an hukumar, matakin na daga cikin kokarin dakile hijira ba bisa ka’ida ba da kuma yaki da manyan laifukan ketare ta iyakokin Najeriya, musamman a yankin Seme.

Hukumar ta sake jaddada matsayarta na rashin sassauci kan safarar mutane da duk wasu laifukan da ke barazana ga tsaron kasa da rayukan al-umma.

Ta kuma ce nasarar aikin ta samo asali ne daga ingantacciyar hadin gwiwa da aka samu tsakanin hukumomin tsaro, tare da alkawarin ci gaba da karfafa tsaron iyakoki a fadin kasa.

Leave a Reply