An Kama Ɗa Kan Zargin Shirya Sace Mahaifinsa A Adamawa

0 447

Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a sace Alhaji Ahmadu a garin Malabu, da ke Ƙaramar Hukumar Fufore. Lamarin ya ja hankalin jama’a saboda yadda aka ce an shirya sace mutumin ne da ɗan gida.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. Ya ce kamen ya biyo bayan wani bincike na sirri da aka gudanar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na yankin.

A cewar sanarwar, rundunar ta samu nasarar ne bayan wani samame da aka kai saboda bayanan sirri, domin dakile ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali a jihar Adamawa.

Wannan samame dai ya biyo bayan sace Alhaji Ahmadu da aka yi a ranar 30 ga watan Janairu, 2026, a Malabu. Rundunar ta ce ta ƙara zage damtse ne bisa umarnin Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Dankombo Morris.

Jami’an tsaron sun kai samamen ne zuwa wani wurin da ake zargin maboyar masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Jera, inda suka kama mutanen uku da ake zargi, tare da taimakon wasu ’yan sa-kai na yankin.

An bayyana sunayen waɗanda aka kama da Lawali Haruna mai shekara 45, Yahaya Ibrahim mai shekara 25, da kuma Da’u Alhaji Ahmadu mai shekara 28. Rundunar ta ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya kasance jinin mutumin da aka sace.

’Yan sanda sun ce waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto Alhaji Ahmadu ba tare da ya ji rauni ba, tare da bin sawun sauran mambobin ƙungiyar. Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomi sahihan bayanai.

Leave a Reply