Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar da Wani Gagarumin Rabon Tallafin Magunguna Da Abinci Mai Gina Jiki A Jihohi 10 Na Arewacin Nijeriya

0 209

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gagarumin rabon tallafin abinci da magunguna da abinci mai gina jiki a jihohin arewacin ƙasa 10 da ke fama da matsalolin jin kai.

Jihohin da za su amfana da wannan tallafi sun haɗa da Borno da Adamawa da Yobe da Benue da Neja da Filato da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma jihar Kebbi.

Yayin ƙaddamar da shirin Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da shirin domin tallafa wa al’umomin da ke fama da talauci a jihohin arewacin ƙasa guda 10.

Yayin da yake jawabi a garin Kasarawa, inda aka ƙaddamar da shirin, gwamnan ya ce shirin wanda shugaban ƙasa kasa Bola Tinubu ya ɓullo da shi, ya zo daidai da zuwan azumin watan Ramadan, lokacin da aka fi buƙatar tallafin.

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar ministan ayyukan jin ƙai da kawar da talauci na ƙasa Dr. Yusuf Tanko Sununu.

Gwamnan ya ce ƙudirin shugaban ƙasar ya yi daidai da muradin gwamnatin jihar na raba wa mabuƙata tallafi.

Kimanin mutum 1,000 ne suka amfana da tallafin kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Tallafin da aka raba ya haɗa da buhunan shinkafa da jarakunan manja da man gyaɗa da wasu nau’ikan abinci masu gina jiki.

Leave a Reply