Kwamitin Ayyuka na Musamman Kan Tashohin Mota Da Filayen Jama’a na Jihar Kano Ya Karbe Magunguna Marasa Inganci
Kwamitin Ayyuka na Musamman kan Tashoshin Mota da Filayen Jama’a na Jihar Kano ya mika magunguna marasa inganci da aka kiyasta kudinsu ya kai naira biliyan daya da rabi ga Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Lafiya ta Jihar Kano domin ajiye su cikin tsaro kafin a lalata su.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Farouk Isa Musa, ya fitar a ranar Laraba. Shugaban kwamitin, Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya ce an kwace magungunan ne daga hannun masu sayarwa a kasuwar Dangwaro, kuma sun hada da jabun magunguna da na bogi da wadanda suka lalace ko suka wuce wa’adin amfani(expired).
Ya tabbatar wa al’umma cewa kwamitin na ci gaba da kokarin kare lafiyar jama’a tare da tabbatar da bin ka’idojin tsaro a fadin jihar.
Ya kara da cewa ana aiki kafada da kafada da shugabannin kasuwanni domin gano da kuma cire duk wasu magungunan da ba su dace ba daga kasuwa.
Ya gargadi ’yan kasuwa da masu sayar da magunguna da su bi doka tare da shawartar jama’a su rika sayen magani daga wuraren da aka amince da su.
Darakta Janar na hukumar, Gali Sule, ya ce karbar wadannan magunguna na nuna kudurin gwamnati na kare rayukan da lafiyar l’umma tare da daukar matakan da suka dace kan masu karya doka.
Daga cikin kayayyakin da aka kwace akwai kwalaye 199 na Benzhexol Hydrochloride BP miligram biyar, kwalaye biyar na Cinbul, Levofloxacin miligram 500, kwalaye uku na Cikatetem mililita 60, kwalaye shida na Betaclox da kuma fakiti 80 na Augmentin gram daya, tare da wasu magunguna daban-daban.