Majalissar Dokokin Amurka Ta Amince Da Kudurin Da Zai Kakaba Takunkumi Kan Wasu Mutane a Nijeriya

0 286

Majalisar dokokin Amurka ta amince da wani kudiri mai suna Accolity Act na shekarar 2026, wanda ke da nufin kakaba takunkumi kan wasu mutane da ake zargi da take hakkin ’yancin addini a Najeriya. Kudirin ya tanadi hana bayar da biza ga waɗanda abin ya shafa tare da daskarar da kadarorinsu da ke ƙarƙashin ikon hukumomin Amurka.

Wannan mataki na daga cikin yunƙurin matsa lamba domin a mutunta ’yancin addini da kare haƙƙin ɗan Adam.

Dokar za ta shafi duk wanda bincike ya tabbatar da hannu a cin zarafin ’yancin addini.

Dan majalisar wakilai Riley Moore daga Jihar West Virginia ne ya sanar da kudirin a ranar Talata tare da hadin gwiwar Chris Smith daga New Jersey, inda aka ambaci tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da wasu kungiyoyin Fulani makiyaya ciki har da Miyetti Allah Cattle Breeders Association da Miyetti Allah Kautal Hore.

Kudirin ya bukaci Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da Ma’aikatar Baitulmali su kakaba takunkumi karkashin dokar Global Magnitsky kan duk wanda aka samu da hannu a take hakkin ‘yancin addini.

Haka kuma ya umarci Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya tantance ko wasu kungiyoyin makiyaya Fulani sun cancanci ayyana su a matsayin kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje bisa dokokin Amurka.

Dokar ta kuma bukaci a rika isar da agajin jin kai a jihohin dake tsakiyar Najeriya ta hannun amintattun kungiyoyin addini da na farar hula tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ayyana Najeriya a matsayin kasar da ke da matukar damuwa kan take hakkin ‘yancin addini a karshen shekarar 2025.

Rahotanni sun ce an dauki wannan mataki ne sakamakon hare-haren kungiyoyin dauke da makamai a yankunan Tsakiyar da Arewa, lamarin da ya kara tsananta muhawara kan ko rikicin yana da nasaba da addini ko kuma matsalar tsaro ce mai sarkakiya.

Gwamnatin Najeriya dai ta musanta cewa rikicin addini ne kadai, tana mai cewa matsalar tsaro ta shafi bangarori da dama, yayin da a watan Disambar 2025 Amurka ta kaddamar da hare-haren sama kan mayakan da ke da alaka da kungiyar IS a Arewa maso Yamma cikin hadin gwiwa da Abuja.

Leave a Reply