Hukumar shige ta fice ta kasa Immigration ta kubutar da wasu mutane 8 da akayi safarar su a jihar Jigawa

0 103

Hukumar shige ta fice ta kasa Immigration ta kubutar da wasu mutane 8 da akayi safarar su a jihar Jigawa

Kwamfitirola hukumar na shiyyar Jigawa Ahmad Dauda Bagari wanda ya tabbatar da kama masu safarar, yace wadanda akayi safarar tasu jam’an hukumar sun kubutar su ranar lahadi yayin da ake kokarin tsallakawa dasu jamhuriyar Nijar ta hanyar Kaya-Daurawa da ke karamar hukumar Roni.

Wanda abin ya sha sun hada da maza biyar da kuma mata uku daga jihohin Abia,Edo, Imo da kuma Ogun.

Ahmad Bagari, ya bayyana wanda akayi safarar tasu yan tsakanin shekara 19 zuwa 54, kuma basu da takardun tafiye-tafiye.

Bagari, ya ce ba’a samu miyagun kwayoyi a kayan su ba.

Ya kara da cewa bayan bincike wadanda abin ya shafa za’a mika ga hukumar da yaki da masu safarar mutane ta kasa NAPTIP domin daukar mataki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: