An saki wasu likitoci guda 2 da aka sace a jihar Cross-Rivers

0 99

An saki wasu likitoci guda 2 da aka sace a jihar Cross-Rivers

Kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar itace ta bayyana saki likitocin biyu a safiyar yau

Shugaban kungiyar a jihar Felix Archibong, shine bayyana hakan ga kamfanin dillacin labarai na kasa NAN, a yayin da yake godewa gwamnan jihar da kuma jami’an tsaro wajen taimakon da suka bayar na sakin likitocin

Ya kuma bayyana cewa likitocin biyu tare da wasu mutane da aka sace sun shaki iskar yanci a yau ba tare da an biya kudin fansa ba.

Sakin likitocin biyu na zuwa kwana guda bayan da kungiyar likitoci ta jihar ta shiga yajin aikin sai baba ta gani sakamakon Garkuwa da ma’aikatan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: