Nasha alwashin kawo karshen Boko Haram idan aka zabe ni a shekarar 2023 – Atiku Abubakar

0 81

Dan takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar ya sha alwashin kawo karshen Boko Haram idan aka zabe shi a shekarar 2023

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin yakin neman zaben sa a Gombe.

Kazalika dan takarar shugaban kasan yayi alkawarin gina hanyoyin da suka hada da jihohin Arewa maso Gabas

Atiku Abubakar,yace  gwamnatin jam’iyyar PDP zata samar da arziki da kuma ayyukan yi ga kasa.

Mai neman kujerar ta shugaban kasa, ya bayyana ce za’a samar da wutar lantarki daga dam din Dakin-Kowa zuwa dukkanin sassan arewa maso gabas

Atiku ya fadawa magoya bayan sa,gwamnatin zata habbaka fannin noma domin tabbatar da noman rani da damuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: