Kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyuka na musamman ya gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed

0 87

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyuka na musamman ya gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed.

Wannan sammacin dai ya shafi zargin cusa Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin shekarar 2023 na ma’aikatar jin kai da kula da ayyukan cigaban al’umma.

Shugaban kwamitin, Yusuf Yusuf ne ya yi wannan kiran a lokacin da ministar harkokin jin kai Sadiya Farouq ta bayyana a gaban kwamitin kare kasafin kudin ma’aikatar ta na 2023 jiya a gaban yan majalissun.

Wani mamba a kwamitin, Ishaku Abbo ne, ya tambayi Sadiya Umar Farouq kimanin Naira biliyan 206 da aka ciwo bashi.

Don haka shugaban kwamitin ya amince da bukatar kiran ministan kudi akan ta bayyana a gaban kwamitin domin yin bayani game da naira biliyan 206.

Leave a Reply

%d bloggers like this: