Rundunar yan sandan Jihar Kaduna ta kubutar da mutane 76 ne a Karamar Hukumar Giwa ta jihar a hannun yan bindiga

0 74

Rundunar yan sandan Jihar Kaduna, ta ce Kimanin mutane 76 ne Jami’an ta suka kubutar a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar a hannun yan Bindigar da suka yi Garkuwa da su.

Kakakin rundunar ASP Muhammad Jalige, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya bayyana cewa Mutanen da Jami’an su suka kubutar sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce yan bindigar sun sace mutanen ne a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa wasu wurare.

Kakakin yan sandan, ya ce Jami’an su ne suka matsawa yan bindigar, wanda hakan ne ya kai ga sakin su, bayan musayar wuta a tsakani.

Haka kuma ya ce sauran hukumomin tsaro ne suka tallafa musu wajen fafatawa da yan bindigar a Dazukan da suke Jihar domin kubutar da mutanen.

Jalige, ya ce har yanzu haka suna cigaba da neman wani Direban Mota da kuma Fasinjoji 2 wanda har yanzu ba’a gansu ba.

Kwamishinan yan sandan Jihar CP Yekini Ayoku, ya yabawa hukumomin tsaro da suka taimakawa Jami’an su wajen aiwatar da aikin tare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: