Girgizar kasa: sama da mutane 162 sun mutu sannan daruruwa sun jikkata a tsibirin Java da ke Indonesiya

0 69

Girgizar kasa ta auku a tsibirin Java da ke Indonesiya, sama da mutane 162 sun mutu sannan daruruwa sun jikkata, a cewar rahotanni.

Masu bincike a Amurka sun ce girgizar kasar mai karfin maki 5.6 ta zabtare aƙalla kilomita 10 na yankunan Java.

Ana iya jiyo girman ɓarnarta har a birnin Jakarta mai tazarar kilomita 100 da yankin. Ana cigaba da aikin kwashe mutane musamman daga manyan dogayen bene.

Jami’ai sun yi gargaɗin yanayin da mutane ka iya shiga, sannan sun ce alkaluman mamata na iya karuwa.

Masu aikin ceto na kokarin ganin yada za su kuɓutar da mutane musamman mata da kananan yara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: