Yan majalisar dokokin Ekiti sun tsige kakakin majalisar jihar kasa da mako guda bayan zabansa

0 80

Yan majalisar dokokin Ekiti sun tsige kakakin majalisar jihar, Gboyega Aribisogan kasa da mako guda bayan zabansa.

Mambobin majalisar 17 daga cikin 25 sun kada kuri’ar goyon bayan tsige Aribisogan daga kujerarsa.

An kuma dakatar da shi har sai baba ta gani a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba.

Sun kuma zabi Olubunmi Adelugba mai wakiltan mazabar Emure a matsayin sabuwar kakakin majalisar.

Arigbisogan ya zargi tsohon gwamnan jihar, Kayode Fayemi da kitsa wani makirci don a tsige shi.

A cewarsa, Gwamna Fayemi na hada kai da wasu yan majalisar dokokin guda bakwai din tsige shi a ranar Litinin.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a gefen taron majalisar kakakin majalisun jihohi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: