Hukumar yansandan kasar nan tace zata duba zargin da kaeyiwa babban jami’inta, Abba Kyari

0 118

Hukumar yansandan kasar nan tace zata duba zargin da kaeyiwa babban jami’inta mai kula fannin fikira Abba Kyari, da ake zarginsa da yin damfara Dalar Amurka miliyan 1 da dubu dari 1.

Hukumar ta kara da cewa zata iya dakatarwa ko rage masa mukami matukar aka kamashi akan zargin da akeyimasa, wajan hada baki da babban dan damfarar nan Ramon Abass wanda akfi sani da Hushpuppi.

Kafin hakan dai hukumar binciken kasar Amurka ce ta zayyana sunan kyari da wasu  mutane 6 da ake zargin su da yin damfara ta kafar sada zumunta na zamani, tare da bayar da umarnin a damke shi.

Bayan hakan ne, shugaban yansanda na kasa Usman Baba Alkali, ya bada umarnin a bibiyi tuhumar da akeyiwa babban jami’in

Leave a Reply

%d bloggers like this: