Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa ta raba kayayyakin aikin zabe ga ofisoshinta na kananan hukumomi

Kwamishinan Hukumar mai kula da kwamitin horas da turawan zabe da daukar ma’aikatan hukumar, Auwal Muhammad Harbo ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a Dutse.

Auwal Harbo yace za a raba sauran muhimman kayayyakin aikin zaben cikin awanni 24 kafin a fara zabe.

A nasa jawabin, jami’in kula da turawan zabe na kananan hukumomi na hukumar Mallam Musa Baderi ya bukaci turawan zaben da su kula da kayayyakin zaben.

A nasa bangaren, shugaban Hukumar Zabe ta jiha, Adamu Ibrahim Roni ya jaddada kudirin hukumar na gudanar da sahihin zabe a jiharnan ba tare da tangarda ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: