Gwamna Badaru Abubakar ya amincewa gwamnatin tarayya da ta karbe tutar kasarnan da tafi kowacce tsaye a Najeriya

0 97

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya amincewa gwamnatin tarayya ta karbe tutar kasarnan da tafi kowacce tsaye a Najeriya.

Tutar ta kasarnan wacce tsayinta ya kai mita 50, an kafa ta a harabar gonar Mallam Alu dake karamar hukumar Birninkudu ta jiharnan.

Gwamnan ya sanar da amincewar a lokacin da yake mayar da martani dangane da bukatar da ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya mika masa bayan duba tutar.

Da yake jawabi, Gwamnan ya godewa ministan bisa amsa gayyata da kalamai masu karfafa gwiwa.

Tunda farko, ministan yace tutar ba wai tafi kowace tsayi bane a Najeriya kadai, kazalika ita ce ta biyu mafi tsayi a nahiyar Afirka.

A cewarsa, za ake kula da tutar a matsayin alamar kishin kasa da hadin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: