Immigration ta tabbatar da cewa an kaiwa Jami’anta hari a jihar Katsina

0 148

Hukumar Shige Da Fice ta Kasa, wato Immigration ta tabbatar da cewa an kaiwa Jami’anta hari a kyauyen Gurai na jihar katsina da Jamhuriyar Niger.

Kwamandan Hukumar na Jihar Jigawa CIS Isma’il Abba Aliyu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, a Dutse a lokacin da yake gabatar da wasu mutanen da ake zargi da laifin safarar mutane.

A cewarsa, garin na Gurai, ya yi kaurin suna a matsayin Cibiyar da ake Safarar mutane daga Najeriya, inda ake tafiya dasu zuwa Jamhuriyar Niger, domin zuwa Birnin Tripoli na Kasar Libya da sauran Kasashen Turai.

Kwamandan hukumar ya ce mutanen garin na Gurai sun kai hari kan Jami’an su da suke bibiyar wasu mutane tun daga Kano, har zuwa garin na Gurai, a ranar Alhamis.

Haka kuma ya ce Mutanen garin sun tallafawa Masu Safarar Mutanen, ta hanyar Farmakar Jami’ansu, a daidai lokacin da Jami’an suke kokarin kubutar da mutane 24 da akayi safarar su.

Sai dai ya ce duk da hakan sunyi nasarar Kama mutum 1 daga cikin masu safarar mutanen, tare da kubutar da mutane 4 da za’ayi safarar su.

Alhaji Isma’il Abba Aliyu, ya gargadi mutanen da suke bakin Iyakar Kasa, su guji tallafawa masu laifin domin tsira.

Kazalika, ya ce hukumar, zata dauki Mataki akan daidaikun mutane, ko kuma Kungiyoyi da suke tallafawa masu aikata Laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: