Mun samu tabbacin cewa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ba shi da lafiya har ya kai ga yana zubar da jini a wani gidan Gyaran Hali a Kano kamar yadda majiyar mu ta PoliticsDigest ta bayyana.

Lauyan na sa Yakubu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, wasu daliban malami ne ke zargin cewa an sanya wa malamin su guba a gidan yarin.

“Ya kasance cikin koshin lafiya kafin a kai shi gidan yari a ranar Litinin bayan da Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da shi”. Lauyan nasa ya fada.

Abduljabbar Kabara dai gwamnatin jihar ta gurfanar dashi a gabanta ne kan zargin yin batanci ga Manzon Allah Muhammad SAW.

An sani cewa Sheik Kabara ya nemi afuwa gafara bayan an kammala muhawara tare da hadakar kungiyar Malaman Kano da gwamnatin jihar ta shirya.

A lokacin muhawarar ya ki amsa tambayoyin da aka gabatar yana mai nuni da cewa lokacin da ka bashi yayi kadan da zai amsa tambayoyin da aka yi masa.

Bayan hakan ne gwabnatin jihar Kano karkashin kulawar jami’an tsaro sukai gaba dashi zuwa gidan kaso kafin wannan rashin lafiya tasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: