Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse ta ce kimanin dalibai dubu 3,657 ta bawa gurbin karatu

0 73

Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Dutse wato FUD, a jiya Juma’a ta ce kimanin Dalibai dubu 3,657 da bawa gurbin Karatu a Zangon Karatun shekarar 2020/zuwa 2021.

Rijistaran Jami’ar Malam Bukar Usman, shine ya bayyana cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Makarantar Malam Abdullahi Yahaya ya rabawa manema labarai a Dutse.

A cewar, Rijistaran, a ranar 2 ga watan Agusta ne, sabbin Daliban zasu  fara Rijistar Zangon Karatu na farko.

Sanarwar ta ce kimanin Daliban dubu 3,234 ne suka samu gurbin Karatu a Jami’ar ta hanyar Jarabawar Jamb, sai kuma mutane 423 da suka sami gurbin karatu ta hanyar shiga Kai tsaye.

Haka kuma ya ce Jami’ar zata fitar da sunayen sabbin daliban rukuni na biyu za zarar hukumar Jamb ta kammala shirye-shirye daukan karin wasu daliban a wannan shekarar.

Sanarwar ta ce tsoffin Daliban Jami’ar zasu fara Rijista daga ranar 16 ga watan Agusta.

Kazalika, sanarwar ta ce kowanne sabon Dalibi zai biya Naira dubu N2,000 kafin karbar takardar samun samun gurbi a Jami’ar wato Admission Letter.

Leave a Reply

%d bloggers like this: