Shafin sada zumunta na X ya bayyana cewa ya kulle shafin mutum 8,000 a Indiya bisa umarnin da ya samu daga gwamnatin ƙasar, a daidai lokacin da rikicin siyasa ke ƙara tsananta tsakanin Indiya da Pakistan.
Waɗannan shafukan sun haɗa da na kafafen watsa labarai na Pakistan kamar Dawn da Geo TV, da kuma na wasu ƴan jarida daga Pakistan.
A wani mataki na ɗan lokaci, X ta kuma dakatar da shafin sashen hulɗa da harkokin gwamnatinta a Indiya kafin ta dawo da shi.
X ya ce wannan mataki na kulle shafukan ba abu ne mai sauƙi, amma an yi hakan ne domin tabbatar da cewa kafar za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga ƴan Indiya.
X, mallakin Elon Musk, ta bayyana cewa tana bincikar duk wata hanya ta shari’a da za ta iya bi don ƙalubalantar wannan umarni.