INEC Ta Bayyana Kudurorinta Kan Hudu Ari, Wanda Ya Bayyana Nasarar Aishatu Binani A Ranar Lahadi Da Ta Gabata

0 63

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a yau ta fitar da wasu kudirori kan sake zaben jihar Adamawa, inda ta ce za a kai rahoton kwamishinan zabe Hudu Ari ga babban sufeton ‘yan sanda, Usman Alkali Baba da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.
Gidan rediyon Sawaba ya bayar da labarin cewa Hudu Ari ya kwace ikon jami’in sanar da sakamakon zabe inda ya sanar da ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben a ranar Lahadi.
A lokacin da Hudu Ari ya bayyana sakamakon zaben, na kananan hukumomi 10 ne kacal cikin 20 aka tattara.
Da ake tashi daga taron shugabaninta akan batun a yau, hukumar ta INEC ta ce za a ci gaba da tattara sauran sakamakon a duk lokacin da jami’in sanar da sakamakon zabe ya tsara.
A halin da ake ciki, ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC, Aishatu Binani, ta bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da ita a matsayin zababbiyar gwamnar jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: