NBS Ta Ce Mata Na Ci Gaba Da Samun Karancin Wakilci A Dukkan Matakan Gwamnati

0 76

Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce mata na ci gaba da samun karancin wakilci a dukkan matakan gwamnati da na mulki.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton kididdiga na hukumar kan mata da maza a Najeriya da aka fitar yau a Abuja.
Rahoton ya kara da cewa, duk da kokarin da ake na inganta gudunmawar da mata ke bayarwa a fagen siyasa da mulki, mata na ci gaba da samun karancin wakilci a kowane mataki da bangaren shugabanci.
Rahoton ya kara da cewa mata su ne kusan rabin wadanda suke zabe.
Rahoton ya ce a Najeriya ba a taba nada mace a matsayin sakatariyar gwamnatin tarayya ba.
Rahoton ya ce tun bayan samun ‘yancin kai mace bata taba zama shugabar kasa ko mataimakiyar shugabar kasa a Najeriya ba.
Rahoton ya ce mafi girman wakilcin mata a majalisar wakilan kasar shine wanda ya kai kashi 7.2 bisa 100 a shekarar 2007 zuwa 2011.

Leave a Reply

%d bloggers like this: