INEC ta gargadi yan takara akan su guji bayar da gudunmawa ko karbar abinda da ya wuce Naira miliyan 50

0 75

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi Daidaikun Mutane, Jam’iyyun Siyasa ko ’Yan takara akan su guji bayar da gudunmawa ko karban gudunmawar da ya wuce Naira miliyan 50 domin gudanar da zabukan 2023.

Wannan dai na kunshe ne a cikin ka’idojin yakin neman zabe, da kudaden da ake kashewa a zaben jam’iyyun siyasa, da ‘Yan takara da masu neman tsayawa takara a zaben 2023 da hukumar ta fitar jiya a Abuja.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da INEC ta amince da sake nada sakatariyar hukumar, Mrs Rose Oriaran-Anthony, a karo na biyu kuma na karshe na shekaru hudu, daga ranar 7 ga watan Disamba, 2022, kamar yadda sashe na 8 na dokar zabe, 2022 ya tanada.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar tare da ka’idojin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: