Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa (JAMB) ta ce za ta gudanar da jarabawar gyara ta 2025 UTME ranar Asabar, 28 ga watan Yuni.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa jarabawar za ta kunshi ɗalibai 5,096 da suka fuskanci matsalolin fasaha da kuma 91,742 da suka kasa halartar jarabawar da aka sake.
Jimillar daliban da za su zauna wannan jarabawa ta gyara a cibiyoyi 183 a fadin kasa sun kai 96,838, yayin da aka sanya wasu a jira.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ɗalibai za su iya fara buga takardar shaidar shiga jarrabawa daga yau Litinin, 23 ga Yuni.