Jihohi goma sha ɗaya a Najeriya na shirye-shiryen fara kiwon dabbobi ta hanyar wuraren kiwo (ranching) domin magance rikicin makiyaya da manoma da ya jima yana haddasa asarar rayuka.
Jihohin da ke cikin shirin sun hada da Lagos da Plateau da Ondo, Zamfara da Bauchi da Delta da Neja da Kano da Jigawa da Nasarawa da kuma Anambra, inda wasu suka riga suka ware filin da za’a gudanar kiwon, yayin da wasu ke kammala tsare-tsaren doka.
A jihar Lagos, hukumomi sun ce suna da doka da ke hana kiwo a fili, kuma sun fara gina wuraren kiwo tare da bai wa kamfanonin masu zaman kansu damar shiga.
Shugaba Tinubu ya danganta rikicin da wani nau’in kwace filaye ne tare da umartar jami’an tsaro da su kama masu hannu a kashe manoma, yayinda mazauna Lagos da dama ke goyon bayan tsarin kiwo a wurare na musamman.