Gwamna Namadi ya yabawa Hadejawa bisa irin tarbar da suka masa a lokacin taron gwamnati da jama’a

0 162

Gwamnan jihar jigawa Umar Namadi ya yabawa Hadejawa bisa irin tarbar da suka masa a lokacin taron gwamnati da jama’a na karamar hukumar da aka gudanar a jiya Lahadi 22 ga watan Yuni.

Gwamnan ya yi wannan yabon ne a jawabin da ya gabatar a lokacin bikin, ya kara da cewa irin tarba da kuma karramancin da aka nuna masa ya nuna a fili cewar Hadejiawa suna cin moriyar gwamnatin jiha

Namadi ya ce zasu yi duba cikin tsanaki akan kundin bukatar aiyuka da KH ta gabatar domin dubawa da kuma yin nazari, sannan ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jiha na cigaba da aiwatar da aiyukan raya kasa a KH Hadejia 

Tun farko gwamnan ya bude wata makaranta da shugaban KH ya samar da kuma wani asibiti da Sanatan jigawa ta gabas, sanata Abdulhamid Mallam Madori ya samar a garin na Hadejia

Gwamnan ajawabinsa a fadar mai martaba sarkin Hadejia, a ziyarar ban girma da ya kai ga mai martaba sarkin gabanin taron na  gwamnati da jama’a, ya ce ana gudanar da taron gwamnati da jama’a ne domin sanar da al-umma aiyukan da gwamnati ta yi da kuma jin bukatun alumma kai tsaye.

Leave a Reply