Jami’an Gwamnatin Saudiyya 5 aka yankewa hukuncin zaman gidan yari saboda wadaka da dukiyar jama’a

0 105

Wasu jami’an gwamnatin Saudiyya 5 aka yankewa hukuncin zaman gidan yari, saboda wadaka da dukiyar jama’a, da cin amanar aiki tare da tara dukiyar haram, a cewar wata sanarwa.

Mutanen 5 sun samu hukuncin zaman gidan yari na tsawon jumillar shekaru 32.

Masu gabatar da kara na gwamnati sun tattara hujjoji 300 akan wadanda ake kara, tare da gabatar da su a gaban kotu, a cewar sanarwar wacce aka buga a shafin kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya.

An kuma umarce su da biyan tara ta kudi sama da Riyal Miliyan 9, kwatankwacin kimanin naira miliyan 867. Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace kudadensu da ke ajiye a bankuna.

Daga cikin wadanda aka yankewa hukunci, akwai wani jami’i wanda aka kama yayin da yake karbar cin hanci domin amincewa da wasu matakai ba bisa ka’ida ba, bayan shiga lamarin yin karya a takardu.

An yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 12, kuma an umarce shi ya biya tarar kudi Riyal Miliyan 1.

Leave a Reply

%d bloggers like this: