Manyan baki daga sassan kasarnan sun halarci daurin auren Ummahani, yar gidan Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Alhaji Mukhatar Abdullahi da Ummahani Badaru Abubakar sun zamanto ango da amarya bayan da suka raya sunar manzo a masallacin Alfurqan dake Jihar Kano, inda aka Cigaba
Gwamnatin Kasar Zimbabwe tace kawo yanzu ta kori kananan likitoci 435 daga aiki a asibitocin gwamnati, saboda shiga haramtaccen yajin aiki. Likitocin na yajin aiki tun farkon watan Satumba, inda suke neman karin albashi tare da inganta yanayin aiki. Kotun ma’aikata a watan Oktoba ta ayyana cewa yajin aikin bai hallata ba, amma sai likotocin […]Cigaba
Ofishin kula da basussuka na kasa yace jumillar bashin da ake bin Najeriya ya kai kudi Naira Tiriliyan 25 da Biliyan 700. Darakta-Janar ta ofishin, Miss Patience Oniha, ita ta bayyana haka yayinda take jawabi ga kwamitin kula da asusun kudaden gwamnati na majalisar wakilai ta kasa a Abuja. Patience Oniha tace basussukan da aka […]Cigaba
Gwamnatin jihar Jigawa zata gina kamfanin sarrafa takin zamani a wani bangare na kokarin habaka ayyukan gona a jiharnan. Manajin Darakta na kamfanin samar da kayan gona na jihar Jigawa, JASCO, Alhaji Rabi’u Khalid Maigatari, shine ya bayyana haka, yayinda ya kai ziyara zuwa gidan Rediyon Jigawa a Dutse. Yace samar da kamfanin sarrafa takin […]Cigaba
Wasu jami’an gwamnatin Saudiyya 5 aka yankewa hukuncin zaman gidan yari, saboda wadaka da dukiyar jama’a, da cin amanar aiki tare da tara dukiyar haram, a cewar wata sanarwa. Mutanen 5 sun samu hukuncin zaman gidan yari na tsawon jumillar shekaru 32. Masu gabatar da kara na gwamnati sun tattara hujjoji 300 akan wadanda ake […]Cigaba
Zanga-zangar gama gari a kasar Iran dangane da karin farashin man fetur ta jawo kame mutane sama da 40, an kuma bayar da rahoton mutuwar wani jami’in dansanda guda, yayinda hukumomin kasar Iran suke gargadi dangane da mayar da martani kakkausa. Masu zanga-zanga sun fita tituna a manyan biranen dake fadin kasar suna adawa da […]Cigaba
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC tace ta rufe gidajen biredi 22 da gidajen pure water 25 yayin zagayen bincike a birnin Maiduguri. Jagoran hukumar a jihar Borno, Nasiru Mato, shine ya bayyana haka yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, jim kadan bayan gudanar da sumamen a Maiduguri. Nasiru […]Cigaba
Hukumar lafiya matakin farko a nan jihar Jigawa tace zata yiwa yara akalla miliyan 1 da Dubu 800 allurar rigakafin kyanda da sankarau a jiharnan. Sakataren zartarwa na hukumar, Dr. Kabiru Ibrahim, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Dutse. Kabiru Ibrahim yace gwamnatin jihar ta samar da isassun allurar domin samun […]Cigaba
Wata jami’a a tsakiyar kasar Isra’ila ta bayar da rahoton cewa kasashen Israila da Jamus zasu assasa wata cibiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa, domin yin bincike akan hanyoyin magance tsufa da tsawaita rayuwa. Bisa la’akari da karuwar dadewa a duniya, gwamnatin Jamus ta yanke shawarar zuba jari a babbar cibiyar wacce zata hada […]Cigaba
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya hannun akan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin jiragen sama na MaxAir, domin jigilar matafiya a kullum, tsakanin Bauchi da Abuja. Da yake jawabi bayan sanya hannu akan yarjejeniyar, gwamnan jihar, Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Baba Tela, yace yarjejeniyar zata bunkasa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya Cigaba