An fara bincike kan kawo karshen tsufa!

0 436

Wata jami’a a tsakiyar kasar Isra’ila ta bayar da rahoton cewa kasashen Israila da Jamus zasu assasa wata cibiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa, domin yin bincike akan hanyoyin magance tsufa da tsawaita rayuwa.

Bisa la’akari da karuwar dadewa a duniya, gwamnatin Jamus ta yanke shawarar zuba jari a babbar cibiyar wacce zata hada da jagorantar manyan masu bincike daga kasashen Israila da Jamus.

Masu binciken za suyi bayani akan tambayoyin kimiyya na kula da hanyoyin tsufa tare da tsawaita rayuwa.

A cewar jami’ar, sabuwar cibiyar zata zama irinta ta farko a duniya, wacce zata mayar da hankali akan sinadarin halitta wadanda suke jawo tsufa, tare da bayyana wannan ilimin wajen tsawaita rayuwar bil’adam bayan sun kwashe shekaru masu yawa, da kuma magance cututtukan dake da alaka da tsufa.

Masu binciken na kasashen Israila dana Jamus na kokarin fahimtar siddabarun tsufa, da kuma yadda za a kula da lafiyar jiki tare da yadda za a magance cututtukan dake da alaka da tsufa kamar yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: