Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya hannun akan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin jiragen sama na MaxAir

0 137

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya hannun akan yarjejeniyar fahimtar juna da kamfanin jiragen sama na MaxAir, domin jigilar matafiya a kullum, tsakanin Bauchi da Abuja.

Da yake jawabi bayan sanya hannu akan yarjejeniyar, gwamnan jihar, Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Baba Tela, yace yarjejeniyar zata bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

Gwamnan ya bayyana sanya hannu a dokar a matsayin babban cigaba, inda ya kara da cewa, hakan zai karfafa jajircewar gwamnati na dabbaka hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, wajen cigaban jihar.

Ya kuma ce, yarjejeniyar zata saukaka damar shiga kasuwanni, da samun kayayyaki, da samar da ayyukan yi, da gidaje da kiwon lafiya, da ilimi, da sauransu.

Janar Manaja na kamfanin MaxAir, Dr. Raymond Omojale, yace kamfanin zai kaddamar da aikin jigilar a ranar 26 ga watan da muke ciki an Nuwamba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: