Gwamnatin Kano za ta gyara titin zuwa sansanin horas da masu yiwa kasa hidima NYSC
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tabbatar da alkawarin gwamnatinsa na gyara titin zuwa sansanin horas da masu yiwa kasa hidima NYSC na dindindin a karamar hukumar karaye ta jihar.
Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnati, Alhaji Usman Alhaji, yayi alkawarinne yayinda ya karbi bakuncin tawagar wakilan hukumar ta NYSC wadanda suka kai masa ziyarar girmamawa.
Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa shirin yiwa kasa hidima, wajen cimma manufar shirin a matsayin babban makami na hadin kai tare da cigaban kasa.
Gwamna Ganduje yace gwamnati na aiki tukuru wajen samar da dukkan hadin kai da goyon bayan da kayan aikin da shirin ke bukata, tare da magance sauran matsaloli a sansanin horas da masu yiwa kasa hidimar.
Tunda farko, a nata jawabin, wakiliya a hukumar, wacce ta jagoranci tawagar, Hajiya Binta Mu’azu, tace sunje kano ne domin duba kayan aiki a sansanin horas da masu yiwa kasa hidimar na dindindin.