Hukumar ruwan sha ta Jihar Jigawa ta mayar da gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 44 A fadin Jihar Jigawa

0 106

Hukumar ruwan sha ta jihar Jigawa ta mayar da gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 44 a fadin jiharnan, cikin shekaru 4.

Manajan Daraktan Hukumar Injiniya Zayyanu Rabiu shine ya sanar da hakan ga manema labarai a ofishinsa.

Yace an mayar da gidajen ruwan ne masu amfani da man gas zuwa masu amfani da hasken rana a tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2019, inda ya kara da cewa daga cikin adadin an mayar da guda 14 zuwa masu amfani da hasken rana a shekarar 2016 da 14 a shekarar 2017 da 8 a shekarar 2018 da kuma 8 a shekarar 2019.

Injiniya Zayyanu Rabiu ya ce hukumar ta samar da sabbin gidajen ruwa masu amfani da man gas guda 13 a fadin jihar nan daga shekara ta 2018 zuwa 2019 inda yace daga cikin adadin an samar da guda 8 a shekarar 2018 da kuma 5 a shekarar 2019.

Manajan Daraktan ya kara da cewa suna da burin kara mayar da gidajen ruwa masu amfani da man gas guda 15 zuwa masu amfani da hasken rana a shekarar 2020 da kuma samar da sabbin gidajen ruwa masu amfani da hasken rana guda 12 a shekarar 2020. Yace za a gudanar da gagarumin aikin samar da ruwansha na kasa na hadin gwiwa da bankin duniya a garin Birnin-Kudu, wanda zai lashe kudi naira miliyan 400.

Leave a Reply

%d bloggers like this: