Mai Dokar Bacci: Dansanda Da Wani Sun Shiga Hannu Bayan Aikata Laifi

0 208

Hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, reshen jihar Yobe, tace ta kama jam’in dan sanda da kuma wani mai safarar miyagun kwayoyi wadanda aka boye sunan su, bisa kama su da kuma samar da kwayoyi Tramodal da nauyin su ya kai kilogram 59 ga mayakan Boko Haram da ke Gwoza a jihar Borno.

Kwamandan Hukumar na jihar Borno Mr Reuben Apeh, a yayin da yake sanar da manema labarai, ya bayyana cewa an kama masu laifin a ranar 7 ga wannan watan na Nuwamba da muke ciki.

Mr Apeh ya sanar da cewa me safarar miyagun kwayoyin ya bayyana cewa yana siyan haramtattun kwayoyin ne daga wajan jam’in jami’in kwastom da ba’a bayyana sunan sa ba a jihar Legas.

Ya bayyana cewa nan bada jimawa za’a mika wadanda ake zargin zuwa kotu.

Kwamandan sai kuma yayi kira ga masu ruwa da tsaki da al’umma da su hada hannu da hukumar wajan ganin an dakile safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: