Za a yiwa yara miliyan 1 da dubu 800 allurar rigakafin kyanda da sankarau a jihar Jigawa

0 104

Hukumar lafiya matakin farko a nan jihar Jigawa tace zata yiwa yara akalla miliyan 1 da Dubu 800 allurar rigakafin kyanda da sankarau a jiharnan.

Sakataren zartarwa na hukumar, Dr. Kabiru Ibrahim, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Dutse.

Kabiru Ibrahim yace gwamnatin jihar ta samar da isassun allurar domin samun nasarar aikin rigakafin na kwanaki 8, wanda aka fara a jiya.

Yayi bayanin cewa kimanin ma’aikatan wucin gadi 5,000 aka dauka domin aikin rigakafin a cibiyoyi 27 da aka ware a jihar.

Sakataren yayi nuni da cewa, manufar hakan shine tabbatar da cewa an yiwa dukkan yara rigakafin cututtukan.

Kabiru Ibrahim daga nan sai ya bukaci iyaye a jiharnan da su kai yayansu zuwa cibiyoyin rigakafin dake garuruwansu, domin yi musu allurar.

Kabiru Ibrahim sai kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki, musamman sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da su taimaka wajen wayar da kan mutanensu wajen cin gajiyar aikin rigakafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: