Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen biredi 22 da gidajen ‘pure water’ 25 a Maiduguri

0 212

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC tace ta rufe gidajen biredi 22 da gidajen pure water 25 yayin zagayen bincike a birnin Maiduguri.

Jagoran hukumar a jihar Borno, Nasiru Mato, shine ya bayyana haka yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa, jim kadan bayan gudanar da sumamen a Maiduguri.

Nasiru Mato yace wasu daga cikin gidajen da aka rufe basu cika ka’idajojin aiki ba, yayinda wasu basu da rijista da hukumar.

Yayi bayanin cewa, duk wajen da aka samu karya doka, hukumar tana yanke hukuncin da ya dace ga wadanda suka saba dokar, domin tabbatar da lafiyar masu sayen kayayyakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: