Manyan Baki Sun Halarci Daurin Auren Ummahani ‘Yar Gidan Gwamna Muhammad Badaru Abubakar

0 122

Manyan baki daga sassan kasarnan sun halarci daurin auren Ummahani, yar gidan Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.

Alhaji Mukhatar Abdullahi da Ummahani Badaru Abubakar sun zamanto ango da amarya bayan da suka raya sunar manzo a masallacin Alfurqan dake Jihar Kano, inda aka biya sadakin kudi Naira dubu 100.

Wata tawaga daga fadar shugaban kasa wacce shugaban ma’aikatan fadar, Malam Abba Kyari, ya jagoranta sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari biyo bayan rashin halartar da yayi sakamakon wasu ayyukan dake gabansa.

Daga cikin tawagar da suka zo daga fadar shugaban kasar akwai babban darakta mai kula da baki, Malam Lawal Abdullahi Kazaure, da mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa, Sabiu Yusf Tunde, da kuma babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar a harkokin yada labaru Malam Garba Shehu.

Itama majalisar dokokin kasarnan ba’a barsu a baya ba, inda ta samu wakilci mai karfi bayan da shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawal ya halarci taron, inda shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Mas’ud Doguwa ya wakilci khakakin majalisar tarayya, sauran yan majalisar da suka fito daga bagaren dattawa da kuma na tarayya da dama ne suka halarci daurin auren.

A wajen daurin auren wanda mukaddashin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Yusuf Gawuna ya kasance mai masaukin baki, Gwamnoni da suka zo sun hada da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, da Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu, da sabon Gwamnan Jihar Bayelsa David Lyon, da Gwamnan Jihar Yobe Maimala Buni, da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da sauran manya da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: